Zusammenfassung der Episode
A wannan makon, shirin namu ya yi duba ne ga guguwar fasahar zamani ta Artificial Intelligence ko kuma AI, da kuma yadda take sauya fasalin yadda ake koyo da koyarwa a makarantunmu. Ko wace makoma ce ke jiran azuzuwanmu na gaba a daidai lokacin da dalibai suka rungumi amfani da manhajoji irin su ChatGPT da Google Gemini? Gudunmowa ko kuma illar da fasahar AI ke da ita ga dalibai na ci gaba da daukar hankalin masana. A yayin da wasu ke kallon ta a matsayin wata babbar dama ta samun ilimi cikin sauki, wasu kuwa na fargabar cewa za ta sanya dalibai lalaci ko kuma ta maye gurbin malamai gaba daya.

Folgen
Yaɗuwar fasahar AI a harkar koyo da koyarwa
GehörtA wannan makon, shirin namu ya yi duba ne ga guguwar fasahar zamani ta Artificial Intelligence ko kuma AI, da kuma yadda take sauya fasalin yadda ake koyo da koyarwa a makarantunmu. Ko wace makoma ce ke jiran azuzuwanmu na gaba a daidai lokacin da dalibai suka rungumi amfani da manhajoji irin su ChatGPT da Google Gemini? Gudunmowa ko kuma illar da fasahar AI ke da ita ga dalibai na ci gaba da daukar hankalin masana. A yayin da wasu ke kallon ta a matsayin wata babbar dama ta samun ilimi cikin sauki, wasu kuwa na fargabar cewa za ta sanya dalibai lalaci ko kuma ta maye gurbin malamai gaba daya.
Matakin sallamar shugabannin makarantu sama da ɗari 4 a Nijar ya haifar da cece-kuce
GehörtShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya maida hankali ne kan matakin sallamar shugabannin makarantu sama da ɗari 4 da gwamnatin Nijar tayi, bayan da ɗaliban makarantun da suke jagoranta na firamari da kuma sakandare suka gaza samun makin da ake buƙata, lamarin da ya sanya ɗiga ayar tambaya kan ko wannan mataki zai haifar da ɗa mai ido ga ɓangaren ilimin ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Yadda ƙarancin malamai ke barazana ga harkar ilimi a yankin Afrika
GehörtShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon zai kai ku kai tsaye zuwa cikin azuzuwan karatu na yankin Afirka ta Kudu da Sahara, yayin da rahoton baya-bayan nan na hukumar UNESCO ya girgiza duniya, inda ya bayyana cewa ana buƙatar ƙarin malamai miliyan Hamsin nan da shekara ta 2030 domin ceto ilimin duniya. Amma abin mamaki da kuma ban tsoro shi ne; kusan miliyan 15 na waɗannan malamai, a nan yankinmu na Afirka ake buƙatarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Yadda ambaliyar ta kassara makarantu da dama a arewacin Najeriya
GehörtShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba halin da makarantu ke ciki ne a Tarayyar Najeriya sakamakon fuskantar matsalar ambaliyar ruwa a sassa daban daban na ƙasar.
Najeriya: saɓanin alƙaluma kan jihar da ɗalibanta ke kan gaba a cin jarabawar NECO
GehörtA yau shirin zai leƙa Najeriya, inda aka samu saɓani ta fuskar alƙaluma a fannin ilimi, bayan fitar da sakamakon jarabawar ƙasa ta NECO na shekarar 2026, gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa jihar ce ta zo ta ɗaya a fadin ƙasar. Sai dai, wani bincike mai zurfi da jaridar Premium Times ta yi, ya musanta wannan iƙirari, inda ta ajiye jihar a matsayi na 31. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...